Barcelona ta soma cire rai daga sayen Haaland, Newcastle na son Anthony Martial - BBC

..

Asalin hoton, Getty Images

Mataimakin shugaban Barcelona Rafael Yuste ya kawar da zancen burin da kulob ɗin ke da shi na sayen ɗan wasan gaban Norway Erling Braut Haaland mai shekara 21 daga Borussia Dortmund a kaka mai zuwa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasan gaban Brazil Neymar mai shekara 29 ya ƙyanƙyasa cewa gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar za ta kasance gasa ta ƙarshe da zai buga inda ɗan wasan gaban Paris St-Germain ɗin ba shi da tabbacin ko yana da sauran ƙarfin da zai ci gaba da taka leda. (DAZN, via Goal)

Akwai yiwuwar Barcelona za ta rabu da ɗan wasan Faransa Ousmane Dembele idan ɗan wasan mai shekara 24 bai sake rattaɓa hannu a kan sabon kwantiragi ba inda kulob ɗin na Sifaniya zai iya sayen ɗan wasan gaban Manchester City da Ingila Raheem Sterling mai shekara 26 domin cike gurbinsa. (Sport - in Spanish)

Sabbin mamallaka Newcasle na tunanin sauya kociyan kulob ɗin Steve Bruce da kocin Leicester City Brendan Rodgers ko kuma kuma da kocin Rangers Steven Gerrard ko kuma tsohon kocin Dortmund Lucien Favre. (Mail)

Haka shi ma tsohon kocin RB Leipzig, Ralf Rangnick na daga cikin waɗanda Newcastle ɗin ke harara a matsayin daraktan wasanni. (Telegraph - subscription required)

.

Asalin hoton, Getty Images

Newcastle za ta nemi ƴan wasan Manchester United huɗu idan aka buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa a watan Janairu, cikin waɗanda ake sa ran za ta nema akwai ɗan wasan gaban Faransa Anthony Martial mai shekara 25 da kuma ɗan wasan tsakiyan Netherlands Donny van de Beek mai shekara 24.

Haka kuma akwai ɗan wasan bayan Ivory Coast Eric Bailly mai shekara 27 da kuma ɗan wasan gaban Ingila Jesse Lingard mai shekara 28. (Mirror)

Juventus za ta yi amfani da ɗan wasan tsakiyan Wales, Aaron Ramsey mai shekara 30 a ƙoƙarin da take yi na kawo ɗan wasan Manchester da Faransa Paul Pogba mai shekara 28 zuwa Turin. (Mail)

Ana alaƙanta Tottenham da ƙoƙarin sayen dan wasan tsakiyan Amurka Weston McKennie mai shekara 23 da kuma ɗan wasan tsakiyan Sweden Dejan Kulusevski mai shekara 21 daga Juventus. (Calciomercato, via Teamtalk)

Alvari Morata

Asalin hoton, Getty Images

Su ma Tottenham na hararar ɗan wasan gaban Sifaniya mai shekara 28 Alvari Morata domin yiwuwar maye gurbin ɗan wasan Ingila mai shekara 28 Harry Kane. A yanzu haka dai Morata na Juventus a matsayin aro daga Athletico Madrid. (Fichajes - in Spanish)

Liverpool sun shirya matsa ƙaimi domin sayen ɗan wasan Wolves Adama Traore, 25. (El Nacional - in Catalan)

Chelsea ta amince da sabuwar kwanitragin ɗan wasan bayan Denmark Andreas Christensen mai shekara 25, inda a yanzu haka ake wasu ƴan gyare-gyare kafin a sanar. (Fabrizio Romano on Twitter)

Ɗan wasan tsakiyan Italiya Marco Veratti mai shekara 28 ya ce yana da niyyar taka leda har abada a kulob ɗinsa na Paris St-Germain. (France Info - in French)

Adblock test (Why?)source https://www.google.com/url?rct=j&sa=t&url=https://www.bbc.com/hausa/labarai-58866390&ct=ga&cd=CAIyGjM5YWU2NzNiY2UyZGJkMGI6Y29tOmVuOlVT&usg=AFQjCNGW2GIZqf0kUXeBZRyIU0N-YzKdNA

0 comments: